Home Labarai Tinubu ya ƙaddamar da motoci masu amfani da gas maimakon fetur

Tinubu ya ƙaddamar da motoci masu amfani da gas maimakon fetur

0
Tinubu ya ƙaddamar da motoci masu amfani da gas maimakon fetur

A yau Litinin ne shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ƙaddamar da kashi na farko na motocin da za su rika amfani da iskar gas, CNG, a fadar shugaban ƙasa dake Villa a Abuja

Motocin da yawansu ya kai guda 20, su ne rukuni na farko da kamfanin haɗa motoci na Innoson ya samar dasu.

Shugaban ƙasar ya katse zaman majalisar zartawa ta tarayya, inda yayi amfani da lokacin wajen ƙaddamar da motocin.

Samar da motocin masu amfani da gas na daga cikin matakan da gwamnatin tarayya ke dauka don rage radadin zafin da janye tallafin mai ya haifar.

Idan za a iya tunawa dai a makon da ya gabata ne, shugaban kamfanin motoci na Innoson, Chief Innocent Chukuma ya gana da shugaban kasa Tinubu.

Bayan ganawar, yayi alkawarin cewa nan bada jimawa ba za a fara amfani da motocin masu amfani da CNG.

Daily Trust