
Shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarnin yin cikakken bincike a ma’aikatar jin-kai wadda Betta Edu ke jagoranta kan zargin badakalar kuɗaɗe.
Ministan yaɗa labaru da wayar da kai, Mohammed Idris shi ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.
Ce-ce-ku-ce ya ɓarke a ma’aikatar ne bayan zargin cewa ministar jin-ƙai Betta Edu ta bayar da umarnin tura kuɗi kimanin naira miliyan 585 zuwa asusun banki na wata mata.
Sanarwar da minista watsa labarun ya fitar, ta ce ta samu labarin abin da ke faruwa a ma’aiktar ta jin-ƙai a karkashin Betta Edu, inda ya ce gwamnati ta kuduri aniyar yin bincike don fito da gaskiya.
“Dangane da abubuwan da ke faruwa a ma’aikatar, shugaban ƙasa ya ba da umarnin gudanar da cikakken bincike domin gano gaskiyar abin da ya faru,” in ji sanarwar.
Idris ya ce gwamnati ta kuduri aniyar bankaɗo gaskiyar lamarin, tare ba da tabbacin cewa za a ɗauki matakin da ya dace don ganin an hukunta waɗanda aka samu da laifi.
Ministan yaɗa labaran ƙasar ya ce za a sanar da sakamakon binciken ga ƴan Najeriya.
Umarnin gudanar da bincike da shugaba Tinubu ya bayar, na na zuwa ne bayan fitar wata takardar biyan kuɗi da ministar ta aike wa ofishin babbar akanta janar da ƙasar, inda a ciki take buƙatar a tura zunzurutun kuɗi har naira miliyan 585, 189,500, don biyan tallafi, a wani ɓangare na tallafa wa masu tsananin buƙatar tallafi a wasu jihohin kasar huɗu.
To sai dai wani abu da ya ja hankali game da biyan kuɗaden shi ne sunan asusun bankin da aka biya kuɗin na wata mata ce mai suna Onlyelu Bridget Mojso.
Tuni dai ofishin babar akanta janar ta ƙasar ya ce ba ya biyan kuɗin gudanar da wani aiki na gwamnati a asusun wani mutum.
BBC Hausa