Home Labarai Tinubu ya dakatar da Halima Shehu a matsayin shugabar ma’aikatar NSIPA

Tinubu ya dakatar da Halima Shehu a matsayin shugabar ma’aikatar NSIPA

0
Tinubu ya dakatar da Halima Shehu a matsayin shugabar ma’aikatar NSIPA

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da dakatar da Halima Shehu a matsayin shugabar hukumar kula da shirin tallafawa marasa ƙarfi ta ƙasa, NSIPA.

Tashar talabijin ta Channels ce sanar da hakan a daya daga cikin shirye-shiryenta da safiyar yauTalata.

A cewar Channels, Tinubu ya bada umarnin dakatar war ta nan take.

Yayin da har yanzu ba a bayyana dalilin da ya sa aka dakatar da Halima Shehu ba, hakan na nuni da sauye-sauye a NSIPA.

Hankali ya kai kan hukumar da ke da alhakin gudanar da muhimman shiri kamar su N-Power da shirin tura kuɗaɗe ga marasa galihu, sakamakon matsaloli da ke fitowa daga cikin ta.

A kwanakin baya ne dai masu cin gajiyar shirin N-Power suka gudanar da zanga-zangar lumana a wasu jihohin kasar saboda gaza biyan su alawus-alawus da gwamnatin tarayya ta yi.

Tinubu ne ya nada Shehu a watan Oktoba 2023, kuma Majalisar Dattawa ta tabbatar da nadin nata a ranar 18 ga Oktoba, 2023.