
Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce magajinsa, Bola Tinubu, ya taka rawar gani sosai tun bayan hawansa mulki watanni tara da suka gabata.
Buhari yayi wannan furuci ne yayin da Tinubun ke shan caccaka a kan matsin rayuwa da wasu manufofin gwamnatin sa su ka jefa al’umma.
Sai dai kuma tsohon shugaban kasar ya ce Tinubu ya taka rawar gani idan aka yi la’akari da yanayin da ake ciki, amma ya tabbatar da cewa Najeriya kasa ce mai wahalar mulka.
Buhari ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin shugaban hukumar kwastam, Bashir Adewale Adeniyi da jami’an gudanarwar hukumar ta NCS a garin Daura na jihar Katsina a karshen mako.
Yayin da yake jawabi ga Adeniyi da tawagarsa, Buhari ya ce Najeriya na da wahala wajen mulki, inda ya yi kira ga ƴan kasar da su jure wa matsalolin tattalin arziki da ake fama da su a kasar, tare da marawa manufofi tsare-tsaren gwamnati mai ci.
“Na gode kwarai da zuwan ku. Na yaba sosai. Ina ganin Tinubu ya na kokari sosai,” in ji Buhari.
“Najeriya tana da sarkakiya sosai. Hakika, babu abin da wani zai iya yi sama da haka. ”
Adeniyi, a nasa jawabin, ya godewa tsohon shugaban kasar kan rawar da ya taka ba a taba ganin irin ta ba wajen goyon bayan dokar NCS ta 2023.