
Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da nadin sabbin sakatarorin dindindin na gwamnatin tarayya guda takwas da za su cike guraben da ake da su a wasu jihohi da shiyyoyin ƙasar a ma’aikatan gwamnati.
Ajuri Ngelale, mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai da bayanai ne ya bayyana hakan a wata sanarwa a jiya Juma’a, inda ya ce an nada sabbin sakatarorin din-din-din ɗin ne bayan da ofishin shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya ya gudanar da aikin zaɓo su.
Sakatarorin su ne: Dr Emanso Umobong Okop – Akwa-Ibom, Obi Emeka Vitalis – Anambra, Mahmood Fatima Sugra Tabi’a – Bauchi, Danjuma Mohammed Sanusi – Jigawa, Olusanya Olubunmi – Ondo, Dr Keshinro Maryam Ismaila – Zamfara, Akujobi Chinyere Ijeoma (Kudu-maso-Gabas)) da kuma Isokpunwu Christopher Osaruwamwen (Kudu-maso-Kudu).
“Shugaban ya yi hasashen cewa sabbin sakatarorin dindindin na gwamnatin tarayya za su yi aiki da kwazo, himma da rikon amana ga kasa wajen gudanar da ayyukansu tare da tabbatar da ingantacciyar hidima ga al’ummar Najeriya,” in ji sanarwar.