
Ɗan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Bashir El-Rufai ya bayyana cewa shugaban kasa Bola Tinubu zango ɗaya tak zai yi a mulkin Najeriya, yana mai cewa taliyar ƙarshe ya ke ci yanzu.
Haka kuma ya kara da cewa shima gwamnan Kaduna, Uba Sani, ba zai wuce zangon farko da ya ke ciki ba, za a wancakalar da shi a 2027.
A wasu rubuce-rubuce da ya rika yi a shafukan sa na X, wanda Premium Times Hausa ta gano, Bashir ya zargi gwamnatin Uba Sani da yi wa mahaifin sa tsohon gwamnan Kaduna, bita da ƙulli da zagon kasa don tozartashi da sunan wai ya handame wasu kuɗaɗen jihar Kaduna har dala miliyan 420.
Ba shir ya ce wasu ne a gefe suke zuga gwamna Una Sani y a yi wa mahaifinsu haka duk da moriyar da ya yi da shi.
Da ya waiwayo kan shugaba Tinubu kuma, El-Rufai ya ce wai don ya yi nasara a lokacin da ya ke gwamnan Legas, hakan ba zai sa ya yi nasara a riƙon Najeriya ba.
Sai dai kuma El-Rufai ya ce shi dai fa ɗi sunan wani ba, amma ya san za a fara cewa da wasu ya ke yi, ” Ni dai ban ambaci sunan kowa ba. Gwamnati ce dai da gaza, kuma za ta kwashi kashin ta a hannun ƴan Najeriya a zaɓe mai zuwa, illa iya ka.