
Daga Abba Ibrahim Wada Gwale
Hukumar kwallon kafa ta duniya wato FIFA, ta fitar da sunayen wadanda za’a zaba don zama fitaccen dan kwallo na duniya.
‘Yan wasan dai sun hada da Cristiano Ronaldo daga Real Madrid kuma dan kasar Portugal; da Lionel Messi daga Barcelona kuma dan kasar Argentina; da kuma Neymar daga Paris St-Germain kuma dan kasar Brazil.
A shekarar da ta gabata Ronaldo ne ya lashe kyautar gwarzon dan wasan duniyar bayan da ya doke Messi da Neymar da kuma Antoine Griezmann na Atletico Madrid.
Ronaldo, wanda a baya ya lashe kyautar sau hudu, ya lashe gasar cin kofin La Liga da kuma kofin zakarun turai a Real Madrid, sannan kuma shi ne ya fi kowanne dan wasa zura qwallo a raga a gasar ta zakarun turai da suka lashe.
Messi, wanda ya fi kowa lashe kyautar, ya lashe ta sau biyar ne. Da Neymar sune abokan karawar Ronaldo bayan da suka lashe kofin Copa del Rey na kasar ta Spaniya.
Sai dai yanzu Neymar ya bar qungiyar, inda a yanzu ya ke taka leda a sabon kulob dinsa na PSG.
Hukumar dai ta kuma fitar da sunayen masu koyarwa guda uku wadanda su ma acikinsu ne za’a zabi wanda ya fi fice. Akwai Zinedine Zidane kocin Real Madrid kuma dan kasar Faransa; da Antonio Conte na Chelsea kuma dan kasar Italiya; sai kuma takwaransa na Juventus shi ma dan kasar Italiya wato Maxililiano Alegri.
Kocin Chealsea Antonio Conte na iya lashe kofin gwarzon koci bayan da ya ja ragamar kungiyar har suka kai ga samun nasarar lashe kofin Premier a kakarsa ta farko a Stamford Bridge.
Shi ma kuwa Zidane zai iya lashe kyautar bayan da ya ja ragamar Real Madrid ta lashe gasar La Liga da kofin zakarun turai.
Shi ma Alegri ya jagoranci Juventus ta lashe gasar Serie A, sannan kuma ya kai qungiyar wasan karshe na cin kofin zakarun turai. Sai dai ya sha kasha daci 4-1 a hannun Real Madrid.
An sake gabatar da mai rike da kambun fitacciyar ‘yar kwallon kafar mata Carli Lloyd a matsayin wacce za ta lashe kofin na bana.