Tsofaffin mayakan Neja Dalta da aka tura su karatu kasar Amurka sun godewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa cika alkawari da yayi na cigaba da biya musu kudin karatu da alawus alawus.

Shirin wanda ke karkashin ofishin mai taimakawa shugaban kasa kan afuwa ga mayakan yankin Neja Dalta ne ya shirya mayar da tsaffin mayakan makaranta a kasashen waje domin cigaba da karatu.

Jagoran daliban da suka samu afuwar Gwamnati kuma aka mayar da su makaranta, Jimmy Iwezu ne ya yi godiyar a madadin daliban da aka tura kasar Amurka.

Bayan haka kuma, Jimmy ya nesanta kansu daga wani gangami da ake shirin yi a birnin Washinton domin nuna gazawar Gwamnatin Buhari.

“Muna mika sakon cikakkiyar godiyarmu tare da jaddada goyon bayanmu ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, musamman kan kokarinsa na ganin an samu zaman lafiya a yankinmu na Neja Delta”

Sannan kuma jagoran daliban yayi godiya da ofishin mai taimakawa shugaban kasa kan yin afuwa ga mayakan na Neja Delta kan kokarin da suke yi na ganin an kyautatawa mayakan da aka mayar makaranta a kasar ta Amurka.