Daga Mansur Ahmed
Al’ummar yankin Arewa a kasar mu Nijeriya lokacin mulkin mallaka da bayan bada mulkin kai sun kasance a wani yanayi da Sarakunan Gargajiya da masu fada aji suka danne talaka da azabtar dashi tamkar bawa a wasu lokutan ma gara bawa kan irin Kama karyar da ake yiwa talaka. Zamanin ya kasance cikin yanayi na danniya da Kama karya da handama da babakere da nauyuka iri-iri na zalunci da aka dankara wa talakawa. Talakawa a lokacin na biyan kudin haraji da jangali da nomau a gonakin masu mulki a kyauta. Wasu lokutan ma in masu mulkin lokacin suka kai rangadi a yankunan dake karkashin su akan tilasta wa magidanci ya bar gidansa da dukkan abunda ya mallaka harma da iyalansa domin saukar dasu da tawagar su!
Malam Aminu Kano ya bayyana ne a tsakiyar lokacin da ake irin wannan zalunci da danne hakkin talaka. Yayi kira ga al’umma dasu bijire tare da kin amincewa da zalunci da kama karyan da akeyi masu tare da mutumta su kamar yan adam masu yanci da martaba. Kafuwar NEPU ke da wuya talakawa suka shiga jam’iyyar babu kama hannun yaro wanda ya jawo tsoro da fargaba ga turawan mulkin mallaka da Sarakunan gargajiya domin akidun NEPU na kira ne ga kawo karshen yadda suke tafiyar da mulkin su na son rai .
Talakawa a lokacin sun amsa kiran NEPU na samun yanci wanda hukumomi su kuma a lokacin suka dauki tsauraran matakai a kansu inda yayi sanadiyar daure tare da azabtar da magoya bayan NEPU. Wasu yan NEPU suka tafi gudun hijira wasu kuma akama sheka dasu barzahu. NEPU karkashin jagorancin Mallam itace jam’iyyar farko a tarihin kafuwar Nijeriya a kasa daya na yunkurin yanto talaka daga mulkin zaluncin fir’aunanci. Mallam Aminu Kano shi ya jagoranci dubban yan gwagwarmayan kwato yanci da wadanda muka sami labarin su da wadanda ma ba’a taba jin su ba muka sami yancin da muke morewa a yanzu. Wasu yan NEPU ma tsire su akayi har suka mutu kamar sannanen labarin Malam Audu Angale. Shi dai an tsire shine a bainar jama’a bisa zargin da akeyi masa na batanci ga Iyayen masu mulki ba tare da gurfanar dashi a gaban Shara’a ba. Haka ma an daura daruruwan yan NEPU ba tare da yi musu Shari’a ba in ma an kaisu gaban Shari’a ba’a basu damar kare kansu kan tuhumar da akeyi masu. Irin wannan zalunci da fin karfi shi yasa wasu yan NEPU in aka kai su gaban alkali sai suce su yan mishan ne domin kotunan basu da hurumin yiwa wanda ba Musulmi ba Shari’a sai a Kai su kotun Nasara inda za’a sake su domin babu shaidun da zasu tabbatar da zargin da akeyi musu.
NASARORIN DA YA SAMU A RAYUWA
Wanne nasarori ya samu a gwagwarmayar sa? Allah ya kaddara masa haddar al-qur’ani Mai girma wadda duk inda zai gabatar da Jawabi da wahala bai kawo aya ya fassara da take da alaka da taron ba, haka Lallai Mallam ya sami gagarumar nasara a gwagwarmayar sa na kawo karshen zalunci. Gwagwarmayar Malam ta tilasta wa Sarakunan gargajiya su sake salon mulkin su tare da kawo karshen nomau kyauta a gonakin masu mulki a kyauta. Ya kuma kawo karshen haraji da jangali. Sannan tsayuwar dakan da Mallam yayi ya baiwa ya’yan talakawa damar samun ilimi zuwa kowanne mataki sannan da rike mukaman siyasa da gwamnati wanda a da ya takaita ne kawai ga gidajen mulki, Yau a Najeriya tun daga kan shugaban kasa har kan wadda yafi kowa kankantar mukami Yayan talakawa ne
A yau a ko’ina a Arewacin Nijeriya mutane na kokarin sanin tare da kare hakkokin su da kundin tsarin mulkin kasa ya basu. Suna kuma shiga cikin harkokin bunkasar dimokaradiya domin cigaban kasar su. A yau akwai yancin fadin ra’ayi ka da walwala wanda masu mulkin mulukiya suka hana al’ummar su a wancan zamanin .
WASU DAGA CIKIN MANYAN ABOKAN GWAGWARMAYAR SA.
1. Malam Sa’adu Zungur
2. Bello Ijumu
3. Musa Kaula
4. Baballiya Manaja
5. Alhaji Adamu Danjaji
6. Magaji Dambatta
7. Mudi Sipikin
8. Malam Abba Mai kwaru
9. Malam Illah Ringim
10. Muhammad Danjani Hadejia
11. Malam Audu Angale
12. Alhaji Dauda Dangalan
13. Hajiya Asabe Reza
14. Hajiya Gambo Sawaba
15. Malam Lawal Dambazau
16. Mrs. Bola Ogunbon
Da sauran su da dama
An saka sunan Malam Aminu Kano a, Filin jirgin saman ƙasa da ƙasa dake kano, Asibitin koyarwa na kano, Aminu Kano Legal, Filin taro na Aminu Kano Triangle A Jigawa, Titin Aminu Kano Way a Kano, Jigawa, Lagos, Bauchi, Kaduna Da Abuja
Ya rasu ya bar mata daya, Aishatu. Wadda Allah ya yiwa rasuwa ranar /22/5/2017 da ’yar sa daya Maryam. Sannan ya bar gida daya da gona. Allah ya jikan Mallam