Tubabben Kakakin Majalisar dokokin jihar Kano, Abdullahi Yusuf Ata

Da sanyin safiyar Litinin din nan ne ‘yan majalisar dokokin jihar Kano, suka tsige kakakin majalisar dokokin jihar Kano Alhaji Abdullahi Ata. Tuni kuma aka maye gurbinsa da tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Kabiru Alhassan Rurum, wanda aka tsige kwanakin baya.