Home Labarai An tsinci gawar dalibar jami’ar Nsukka a cikin kwata

An tsinci gawar dalibar jami’ar Nsukka a cikin kwata

0
An tsinci gawar dalibar jami’ar Nsukka a cikin kwata

Hukumomi a Jami’ar Nsukka sun tabbatar da mutuwar wata ɗaliba ƴar aji ɗaya da aka gano gawar ta a magudanar ruwa a ranar Juma’a, 5 ga watan Yuli.

An samu gawar marigayiyar mai suna Favor Okenyi da ke karatu a sashen nazarin kimiyyar aikin likita a kusa da filin wasa na Akanu Ibiam a cikin harabar jami’ar.

A wata sanarwa da ya fitar a jiya Lahadi a Nsukka, mukaddashin jami’in hulda da jama’a na jami’ar, Okwun Omeaku, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce mazauna cikin jami’ar sun yi matukar kaɗuwa da alhinin mutuwar matashiyar ɗalibar.

“A halin yanzu ana gudanar da bincike kan lamarin da ke tattare da mutuwar wanda zai taimaka wajen gudanar da bincike tare da zakulo wadanda suka aikata wannan mummunan aiki,” in ji shi.