Tsohon Gwamnan jihar Kebbi, Saidu Usman Nasamu Dakingari

 

 

Tsohon Gwamnan jihar Kebbi, Alhaji Saidu Usman Nasamu Dakingari da yayi Gwamnan jihar Kebbi shekara 8 karkashin jam’iyyar PDP da mataimakinsa, Aliyu Ibrahim a ranar Juma’a suka bayyana komawarsu jam’iyyar APC daga PDP.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN, ya ruwaito cewar, akwai da dama daga cikin jigajigan jam’iyyar PDP a jihar Kebbi da suka tsallaka zuwa jam’iyyar APC, da suka kunshi tsohon Sakataren Gwamnati, Rabiu Kamba, tsaffin ‘yan majalisar wakilai ta kasa Sani Kalgo, Abdullahi Dan-Alkali, Haruna Hassan da kuma Halima Tukur.

A lokacin da yake zantawa da manema labarai a Birnin Kebbi a ranar Juma’a, Gwamnan jihar Kebbi mai ci, Atiku Abubakar Bagudu ya bayyana wannan komawa APC da tsohon Gwamnan yayi a matsayin wani cigaba na musamman a jihar.

“Muna cikin farin ciki da kuma maraba lale da tsohon Gwamna a APC, kuma hakan ya kara nuna ana cewar Jihar Kebbi ta hade waje guda”

“Dalilin wannan hadu tamu, bai wuce mu ciyar da jihar mu da kasamar Najeriya gaba ba, ba mu da wani fata, face na cigaban jiharmu da kuma kasarmu baki dayanmu”

Shima a lokacin da yake tofa albarkacin bakinsa, Antoni janar na kasa kuma ministan Shariah, Abubakar Maalami, yace komawar tsohon Gwamnan Kebbi APC abu ne da aka nuna hikima a ciki.

“Muna fatan duk wani mahaluki a jihar Kebbi a ko ina yake, day a fito ya taimaki wannan hazikin Gwamna namu Abubakar Bagudu domin ciyar da wannan jihar tamu gaba”

“Gwamnatin tarayyar Najeriya tana yin iyakar kokarinta, wajen habaka tare da bunkasa tattalin arzikin Najeriya, kuma Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari na yin kokari matuka akan sha’anin tsaro, gigginan manya da kananan hanyoyi a ko ina, da kuma batun inganta samar da wutar lantarki”.

Ministan ya bukaci sabbin ‘yan jam’iyyar APC din das u yi amfani da kwarewarsu wajen taimakawa Gwamnan mai ci, wajen bunkasar jihar Kebbi, dama najeriya baki daya.

Da yake Magana a madadin wadan da suka koma APC, tsohon mataimakin Gwamnan jihar Kebbi Ibrahim Aliyu, yace sun dangwarar da jam’iyyarsu ta PDP suka dawo jam’iyyar APC bad an komai ba sai don su ciyar da jihar Kebbi gaba.

“Najeriya na bukatar zaman lafiya, mu kuma a jihar Kebbi muna bukatar cigaba da kuma bunkasar jiharmu, mun dawo jam’iyyar APC domin hada karfi da karfe wajen ciyar da jiharmu gaba, kuma babu abinda zai bayar da dammar hakan illa mu koma APC”.

 

NAN