Marigayi tsohon mataimakin Shugaban kasa Cif Alex Ekwueme

Tsohon mataimakin Shugaban kasa a jamhuriya ta biyu karkashin jagorancin Alhaji Shehu Shagari, Alex Ekwueme ya mutu a kasar Ingila sakamakon jinya da yayi fama da ita.

Idan ba’a manta ba, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin a fitar da Ekwueme zuwa kasar Burtaniya domin jinyarsa a can, inda a kasar yace ga garin ku nan.