
Alhaji Shehu Minjibir, tsohon Shugaban Ma’aikatan Jihar Kano, ya rasu.
Minjibir ya rasu a yau Juma’a, kamar yadda ƙanin sa, Sani Shehu Minjibir ya sanar a madadin iyalin marigayin.
Sai dai ba a baiyana sanadiyar rasuwar ta sa ba, amma dai za a yi jana’izar sa a Masallacin Juma’a na Alfirqan da ke titin Alu Avenue, Nassarawa GRA a jihar Kano bayan sallar Juma’a.
A 2023 ne Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya naɗa marigayin a matsayin Shugaban kwamitin binciken daukar ma’aikata sama da dubu 10 ga gwamnatin tsohon gwamna, Abdullahi Umar Ganduje ta yi.