Tsohon Shugabana kasa Ibrahim Badamasi Babangida

A ranar Alhamis da misalin karfe 12 na rana, tsohon mataimakin Shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar ya isa gidan tsohon Shugaban kasa Ibrahim Badamasi Babangida dake kan tsauni. Ba dai a san me wannan ganawa tasu take nufi ba.

Amma tuni masu fashin bakin siyasa suka ce, ganawar watakila na da alaka da komar Atiku Abubakar jam’iyyar PDP da batun fidda wanda zai yiwa PDP din takarar Shugaban kasa. Idan ba’a manta ba a cikin makon nan ne, dai Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana komawarsa jam’iyyar PDP a sakatariyar jam’iyyar dake Abuja.

Atiku ABubakar ya fice daga jam’iyyar APC wadda ya taimakawa ta kafa Gwamnati a 2015.