
Tsohon shugaban kungiyar ƴan kasuwar Kantin Kwari, Alhaji Sharif Sagiru ya rasu.
Ya rasu yana da shekaru 61 a jihar Kano.
Daily Nigerian Hausa ta jiyo cewa ya rasu ne a daren jiya Talata bayan gajeriyar rashin lafiya.
Wata majiya ta shaidawa wannan jarida cewa marigayi Sharu ya halarci taro a gidansu a jiya Talata da rana kafin rasuwarsa da yamma.
Ya rasu yana da mata 2 da ‘ya’ya 13.
Tuni dai aka binne marigayin a makabartar Dandolo da ke Kano.