Home Labarai Tsohon shugaban majalisar wakilai, Ghali Na’Abba ya rasu

Tsohon shugaban majalisar wakilai, Ghali Na’Abba ya rasu

0
Tsohon shugaban majalisar wakilai, Ghali Na’Abba ya rasu

Tsohon majalisar wakilai, Ghali Umar Na’Abba ya rasu da sanyin safiyar yau Laraba a Abuja.

Wata majiya daga iyalin marigayin ta shaiadawa wa wakilin jaridar DAILY NIGERIAN cewa tsohon dan majalisar ya rasu ne a wani asibiti a Abuja bayan gajeruwar rashin lafiya.

An haifi Na’Abba ne a gidan Umar Na’Abba, dan kasuwa a Tudun Wada, cikin birnin Kano, a ranar 27 ga Satumba 1958.

Ya samu digirin farko a fannin kimiyyar siyasa a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria a 1979.

Ya yi karatun farko a makarantar firamare ta Jakara Kano inda ya samu shaidar kammala karatunsa na farko a 1969.

Daga nan ya halarci Kwalejin Rumfa da ke Kano don samun shaidar kammala karatunsa na sakandare, sannan kuma ya yi makarantar share fage ta Kano tsakanin 1974 zuwa 1976, kafin ya samu gurbin shiga Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya a watan Oktoba, 1976.

Ya kammala karatun digiri na biyu akan Jagoranci da shugabanci na gari a Makarantar Gwamnati ta Kennedy, Jami’ar Harvard ta Amurka a 2004.