Home Labarai Tsohon ɗan takarar shugaban matasa na jam’iyyar APC ya koma PDP

Tsohon ɗan takarar shugaban matasa na jam’iyyar APC ya koma PDP

0
Tsohon ɗan takarar shugaban matasa na jam’iyyar APC ya koma PDP

Tsohon ɗan takarar shugaban matasa a jam’iyyar APC, Bashir Suwaid ya sanar da ficewa daga jam’iyyar zuwa abokiyar burminta PDP.

A taron manema labarai da ya yi a Kano a jiya Lahadi, Suwaid ya alakanta ɗaukar matakin da rashin jan matasa a jiki da jam’iyyar APC ke yi.

Suwaid, ya kuma bayyana cewa ya koma jam’iyyar hamayya ta PDP wacce ya ce ita ce tafi bai wa matasa damammaki.

“A matsayi na na tsohon ɗan takarar kujerar shugaban matasan jam’iyyar APC na ƙasa, na ga yadda aka mayar da gogaggun ‘yan siyasa irina saniyar ware a cikin jam’iyyar. Ba a ba mu damar ba da gudummawar ƙwarewa da iliminmu don ci gaban jam’iyyar ba.

” Wannan rashin tafiya da mu da rashin sanin makamar aiki na gudanar da tafiyar da Jam’iyyar da rashin yadda da irin basirar da muke da shi ya sa na yi imani cewa jam’iyyar APC ba ita ce wurin da ya dace na ci gaba da tafiya ta siyasa ba.

“Saɓanin haka, jam’iyyar PDP ta bambanta wajen janyo mutane da haɗa kan su, da tuntuɓa wanda babu shi a jam’iyyar APC. Ina da ƙwarin gwuiwa da kyakkyawar zato ga ɗan takarar Shugabancin Ƙasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, Wazirin Adamawa. Gogewarsa a siyasa, da kyawawan halayen sa na jagoranci, da jajircewarsa wajen tabbatar da haɗin kai da cigaban Najeriya, shi ya sa ya zama zaɓi mafi dacewa da zai jagoranci ƙasarmu daga ƙalubalen da take fuskanta”.

Sannan ya sanar da cewa ya kafa sabuwar ƙungiya mai taken “PDP Jirgin Fiton Al’umma” don bada tashin gudunmawar ga jam’iyyar har ta kai ga samun nasarori a zaɓen 2027.

“Don bada gudunmawa ta, na kafa wata Ƙungiya na goyon baya mai suna “PDP JIRGIN FITON AL’UMA” domin yin aiki tuƙuru domin nuna goyon baya ga Alhaji Atiku Abubakar da kuma Jam’iyyar mu ta PDP mai albarka a zaɓe mai zuwa. Za mu yi aiki ba dare ba rana don isar da saƙon ɗumbin alheri da canjin da Maigirma Wazirin Adamawa Alhaji Atiku Abubakar zai samar ga al’ummar Najeriya.”

Bashir Suwaid ya kuma ce yana da yakinin cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar zai zamo waraka ga Nijeriya idan ya samu dama