Categories
Labarai

Tun bayan zaben 2015 Buhari ya yi watsi da mijina – Sanata Oluremi Tinubu

 

Hassan Y.A. Malik

Uwargidan tsohon gwamnan jahar Lagos kuma jigo a jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, sanata Oluremi Tinubu ta zargi APC da gwamnatin Buhari da yin watsi da maigidan ta duk da rawar da ya taka a zaben da ya gabata.

A wata hira da aka yi da ita a gidan talabijin na Continental a jiya Litinin, Remi wacce sanata ce mai wakiltar Lagos ta tsakiya ta ce maigidan ta ya yi wa Buhari kamfen sosai, kamar yadda ita ma ta yi. Ta ce amma sai da ta kai da bakinta ta cewa maigidan na ta ya ajiye batun Buhari saboda yadda aka yi watsi da lamarin shi bayan ya ci zabe.

Sai dai sanatar ta ce duk da sukar da gwamnatin sa ta ke fuskanta a yanzu, ta san cewa Buhari mai gaskiya ne, babu dan takara kamar shi, kuma talakawa suna bayan shi, sai dai ko idan mulki ya sauya shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *