Alhaji Lai Mohammed Ministan yada labarai na Najeriya

Ministan yada labarai da al’adu, kuma kakakin Gwamnatin Najeriya Alhaji Lai Mohammed, yace tunda yake a rayuwarsa ta duniya bai taɓa yin karya ba. Alhaji Lai, ya bayyana haka ne  ya yin da yake zantawa da manema labarai a Legas.

Ministan ya kalubalanci duk masu cewar shi makaryaci ne da su zo da hujja kwakkwara da zata tabbatar da inda yayi karya a dukkan kalaman da yayi a baya.

“Tunda uwata ta haifeni ban taba shara karya ba, akwai dalilai guda biyu da yasa na tsolewa ‘yan adawa ido suke min sharrin ni makaryaci ne. Na kasance muryar ‘yan adawa a baya, wannan yasa PDP ba zata taba yin min afuwa ba, kuma ina zaton ba zasu taba yi min gafara kan adawar da na yimusu ba”.

“Sun ganin cewar, maganganu na da adawata a garesu, na daga cikin abinda ya janyo musu koma baya, shi yasa suke min kallon wanda ya lalata musu al’amura, wanda sam ba  haka bane kokadan”.

“Amma dai duk da haka, nayi abinda nayi. Yanzu kuma, ni ne mai magana da yawun Gwamnati, wannan yasa su a wajensu, duk wani abu da ya fito daga bakin Lai Mohammed, to tabbas shararata yayi”.

“Mahaifina, shi ne ya radamin sunan LAI wanda yayi kama da kalmar turanci ta LIE wadda ke nufin karya ko makaryaci, shi yasa abu ne mai sauki a wajensu, su juya ma’anar sunana ta koma makaryaci. Amma dai ni ban damu ba, abinda kullum nake kalubalantarsu, shi ne, su zo da hujja tabbatacciya inda nayi karya, ko kuma wata magana wadda nayi da ba haka take ba”.

“Na san ba zasu yadda da ni ba, yanzu ma zasu ce wannan maganar da nayi karya ce. Amma dai in batu ake yi na magana da hujja, ni ban taba yin karya ba, kuma ina da hujja, ko mutum ya yarda ko kada ya yarda, amma abu ne da ba zaka taba daukewa daga gare ni ba”.

Jaridar Vanguard ce ta ruwaito daga Daily Post.