Shugaban hukumar 'yan sanda ta kasa, Ibrahim K. Idris

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya umaci Sufeton ‘yan sanda na ƙasa, Ibrahim K. Idris da ya koma jihar Bunuwai da aiki domin dawo da doka da oda da kuma tabbatar da zaman lafiya a jihar, a sakamakon mummunan rikicin da ya kaure tsakanin fulani makiyaya da manoma.

Shugaban ya bayar da wannan umarni ne a ranar litinin da daddare, a sanarwar da kakakin rundunar ‘yan sanda ta kasa Jimoh Moshood ya bayar.

Umarnin dai ya zo ne a daidai lokacin da ake kara samun hasarar rayuka wanda Fulani ke yin kisan kan mai uwa da wabi a yankin karamar hukumar Guma da kuma Logo duk a jihar ta Bunuwai.

A sabida cika wannan umarni, tuni sifeton ‘yan sanda na kasa, tare da wata tawagarsa suka koma jihar ta Bunuwai domin tabbatar da an maido da bin doka da oda a yankunan da ake fama da wannan tashin hankali.

Ko a ranar lahadi da ta gabata, rundunar ‘yan sanda ta kasa ta tura wata tawagar ‘yan sanda kwantar da tarzoma zuwa wannan yanki domin dawo da zaman lafiya a inda rikicin ya shafa.

Haka kuma, rundunar ‘yan sanda ta kasa ta tura da wata tawagar kwararrun jami’an tsaro domin tabbatar da dawo da dawwamammen zaman lafiya a yankin.

“A sabida haka, rundunar ‘yan sanda ta kasa ba zata yi kasa a guiwa ba wajen ganin ta sanya kafar wando da duk wani mai shirin kawo zaman zullumi da haifar da tarzma ba, a shirye rundunar ‘yan sanda ta kasa take, tabi duk inda masu tayar da wannan tashin hankali suke domin taga ta kamo su ta hukunta su, hukumar ‘yan sanda ba zata zura ido wasu tsirarun mutane suna kawo zaman zullumi a tsakanin jama’a ba. Dile ne mutane subi doka a wadannan yankuna da abin ya auku”

A wata ganawa ta musamman da aka yi a Abuja, wadda sufeton da kansa ya halarta tare da Gwamnonin jihohin Bunuwai da Taraba da Filato da Nassarawa da Adamawa da Neja da kuma Kaduna, tare da Ministan kula da harkokin cikin gida Abdulrahman Dambazau, an tattauna hanyoyin da za’a bi domin magance wannan rikici na manoma da makiyaya.

A lokacin da yake yiwa manema labarai jawabi, Gwamnan jihar Bunuwai Ortom Samuel yace akwai kalubale babba akan Gwamnatin tarayya da kuma rundunar ‘yan sanda ta kasa wajen ganin tayi abinda ya dace domin dawo da doka da oda cikin gaggawa.

Mista Ortom, wanda suka yi wannan ganawa tare da tawaransa na jihar Taraba Darius Ishaku, sunki bayyana irin dabarun da zasu yi aiki da su domin shawo kan wannan rikici na manoma da makiyaya, a cewarsa, wannan abi abu ne da babu bukatar sai an sanar da al’umma irin hanyoyin da za’a bi domin samar da zaman lafiya.

“Kamar yadda kuke gani, dukkan Gwamnonin da suke da makamanciyar irin wannan matsalar a jihohinsu, sun hallara anan domin tattauna hanyoyin magance matsalar. Mun tattauna kuma mun cimma matsaya, mun kalli matsalolin tare da dukkan jami’an tsaro mun kumma gamsu da hanyoyin da aka kawo don magance su”

“Babban abinda kowa ya amaince da shi shi ne, kisan rai ko ta wacce hanya ce, abune da ba zamu taba yarda da shi ba. Kuma jami’an tsaro zasu fuskanci wadan da suke da hannu kan wadannan kashe kashe tare da tabbatar da cewar an hukunta su”

“Babu wani dalili da zai sanya a siyasantar da rayuwar al’umma; wannan wani abu ne da ya shafi dukkan ‘yan Najeriya baki daya domin mu hada hannu muga mun kawo karshen irin wannan kisan ta’addanci” Inji Gwamna Ortom.

Sannana kuma, Gwamnonin sun amince cewar, dole ne ‘yan Najeriya su guji yin kalaman batanci ga junansu, wanda sune suke iza wutar irin wannan rikici.

NAN