23.1 C
Abuja
Tuesday, February 7, 2023

DA ƊUMI-ƊUMI: APC ta ɗage fara yakin neman zaɓe sai baba-ta-gani

Must read

 

 

 

Kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban kasa na jam’iyyar APC ya ɗage fara yakin neman zaben da aka shirya ƙaddamar wa a gobe Laraba.

Darakta Janar na kwamitin yakin neman zaben Tinubu/Shettima, kuma gwamnan jihar Plateau, Simon Lalong ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a yau Talata.

A cewarsa, an yi hakan ne domin daidaita jadawalin lokaci da jadawalin ayyuka ne domin yai daidai da harkokin duk masu hannu a cikin yakin neman zaben don samun nasararsa.

A cewarsa, nan ba da jimawa ba za a sanar da sabon lokacin da za a fara yaƙin neman zaɓen.

Sanarwar ta ce; “A tuna cewa tun da farko mun shirya tattaki da addu’o’in zaman lafiya a ranar Laraba, 28 ga Satumba, 2022, don fara yakin neman zaben shugaban kasa na 2023 a hukumance. Mun kuma sanar da cewa mambobin kwamitin yakin neman zaben sun kai rahoto a hedikwatar yakin neman zaben a ranar domin karbar wasikun naɗi.

“Duk da haka, saboda faɗaɗa jerin sunayen don samun karin masu ruwa da tsaki da bukatun cikin gida a APC, mun yanke shawarar daidaita jadawalin wadannan ayyuka domin tabbatar da cewa kowa yana cikin jirgin kafin a fara ayyukan a hukumance. Saboda haka, ayyukan da aka sanar a baya na ranar 28 ga Satumba ba za su ci gaba da kasancewa ba

“A matsayinmu na jam’iyya mai mulki kuma mafi inganci a Najeriya, mun fahimci sadaukarwa da fahimtar dimbin mambobinmu wadanda suka fi son sadaukar da kansu don wannan gagarumin aiki da ke gabanmu. Hakan kuma ya nuna irin tsananin soyayyar da ‘ya’yan jam’iyyar ke yi wa ’yan takararmu

“Za a sanar da sabon kwanan wata da jadawalin abubuwan da za su faru nan ba da jimawa ba”.

More articles

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Latest article

- Website Designed By DEBORIAN.COM, a Nigerian Web Designer and Web Developer -