
Rundunar ƴansanda a babban birnin tarayya Abuja ta tabbatar da cafke wani mai suna Chinaza Phillip da ya yi kaurin suna wajen garkuwa da mutane a Abuja.
Daily Trust ta ruwaito yadda aka kama Phillip a Kaduna yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa jihar Kano tare da yaran sa da kuma wadanda ya yi garkuwa da su a ranar Alhamis.
An yi musayar wuta mai zafi tsakanin yaran Phillip da ƴansanda, lamarin da ya kai ga ceto Segun Akinyemi, wani mazaunin Abuja, wanda aka yi garkuwa da shi a lokacin da yake tuki bayan ya baro gidansa a ranar Laraba.
Masu garkuwa da mutanen na dauke da Akinyemi ne daga Abuja zuwa jihar Kano a lokacin da ƴansanda suka yi awon gaba da su, kamar yadda jami’in hulda da jama’a na ƴansandan Kaduna, ASP Mansir Hassan ya bayyana.
A ranar Juma’ar da ta gabata ne Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya sanar da kame wasu masu bads bayanan sirri ga masu garkuwa da mutane.
Wike ya bayyana haka ne a yayin wani taro da masu ruwa da tsaki da suka hada da mazauna garin Gwagwalada da ke karamar hukumar Gwagwalada ta yankin.
Ya sha alwashin bin diddigin masu garkuwa da mutanen da masu ba su bayanan sirri.