Home Labarai DA ƊUMI-ƊUMI: Kotu ta soke dokar da ta rushe masarautu a Kano

DA ƊUMI-ƊUMI: Kotu ta soke dokar da ta rushe masarautu a Kano

0
DA ƊUMI-ƊUMI: Kotu ta soke dokar da ta rushe masarautu a Kano

Babbar Kotun Taraiya dake zaman ta a jihar Kano ta soke dokar da ta rushe masaurutun Kano ta kuma dawo da Sarki Muhammadu Sanusi ll, wanda Ganduje ya cire a 2020.

Aminu Babba Danagundi, the Sarkin Dawaki Babba ne ya shigar da ƙara, ya na kalubalantar sabuwar dokar.

Da ya ke yanke hukunci a yau Alhamis, Alkalin kotun, Abdullahi Muhammad Liman ya soke dokar inda ya bada umarnin a dawo da masarautun.

A cewar alkalin, gwamnatin Kano, wacce ake kara tana sane da umarnin da kotun ta bata amma ta rife ido ta aiwatar da dokar.

Alkalin ya ce ya yi amfani da ƙarfin ikon sa wajen tilasta gwamnatin Kano ta bi umarnin kotun.