Home Labarai DA ƊUMI-ƊUMI: Kotun Daukaka Ƙara ta dawo wa da Gwamnan Nassarawa kujerar sa da tirabunal ta ƙwace

DA ƊUMI-ƊUMI: Kotun Daukaka Ƙara ta dawo wa da Gwamnan Nassarawa kujerar sa da tirabunal ta ƙwace

0
DA ƊUMI-ƊUMI: Kotun Daukaka Ƙara ta dawo wa da Gwamnan Nassarawa kujerar sa da tirabunal ta ƙwace

Kotun daukaka kara da ke Abuja ta soke korar gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa da tirabunal ta yi.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana Gwamna Abdullahi Sule na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben watan Maris, amma David Ombugadu na jam’iyyar PDP ya garzaya kotun tirabunal.

A cewar INEC, Sule ya samu kuri’u 347,209 inda ya doke abokin hamayyarsa na kusa, wanda ya samu kuri’u 283,016.

Sai dai a hukuncin da tirabunal ta zartas a ranar 2 ga Oktoba, ta soke zaben Sule tare da tabbatar da Ombugadu a matsayin wanda ya yi nasara.

Amma Sule, ta hannun lauyansa, Wole Olanipekun (SAN), ya roki kotun daukaka kara da ta soke hukuncin da kotun ta yanke, ta kuma ba da damar daukaka kara.

Sai dai kuma a yau Alhamis ne kwamitin alkalai mai mutane uku suka yanke hukuncin cewa tirabunal ta jihar Nasarawa ta yi kuskure wajen yanke hukuncin cewa Sule bai samu rinjayen kuri’un da aka kada a zaben ba.

Daga nan ne kotun daukaka kara ta yi watsi da hukuncin da kotun ta yanke tare da tabbatar da sake zaben Sule a matsayin gwamnan jihar Nasarawa.