Home Labarai DA ƊUMI-ƊUMI: Kotun Daukaka Kara za ta yanke hukunci kan zaɓen Kano gobe

DA ƊUMI-ƊUMI: Kotun Daukaka Kara za ta yanke hukunci kan zaɓen Kano gobe

0
DA ƊUMI-ƊUMI: Kotun Daukaka Kara za ta yanke hukunci kan zaɓen Kano gobe

Kotun daukaka kara ta sanya gobe Juma’a, da karfe goma na safe a matsayin rana da lokacin da zata yanke hukunci a kan zaben gwamnan Kano.

Wannan bayani na kunshe cikin sakon da kotun ta turawa lauyoyin jam’iyyar NNPP a yau Alhamis, kamar yadda sakataren yada labarai na gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya fitar a wata sanarwa.