
Kungiyar kwadago ta ƙasa, NLC ta ayyana yin zanga-zanga ta kwanaki biyu a fadin kasar a ranakun 27 da 28 ga watan Fabrairu.
Joe Ajaero, shugaban NLC ne ya bayyana haka a yayin wani taron gaggawa, wanda aka gudanar a yau Juma’a.
Ajaero ya ce an dauki matakin gudanar da zanga-zangar ne bayan cikar wa’adin kwanaki 14 da aka baiwa gwamnatin tarayya kan ta magance wahalhalun da kasar ke fuskanta.
NLC ta bada wa’adin ne domin a matsa wa gwamnatin Najeriya don ta magance wahalhalun da ‘yan Najeriya ke fuskanta a halin yanzu.