Home Labarai Da Ɗumi-Ɗumi: Majalisar zartarwa ta ƙasa ta amince a siyarwa Dangote ɗanyen mai da Naira ba Dalar Amurka ba

Da Ɗumi-Ɗumi: Majalisar zartarwa ta ƙasa ta amince a siyarwa Dangote ɗanyen mai da Naira ba Dalar Amurka ba

0
Da Ɗumi-Ɗumi: Majalisar zartarwa ta ƙasa ta amince a siyarwa Dangote ɗanyen mai da Naira ba Dalar Amurka ba

Daga Salisu Hamisu Ali

Majalisar zartarwa ta ƙasa ta amince da a siyarwa da matatar mai ta Dangote ɗanyen mai da kuɗin Naira maimakon Dala.

Shugaban hukumar tattara haraji ta tarayya FIRS, Zacch Adedeji ne ya bayyana hakan bayan taron majalisar zartarwar a yau Litinin.

Da yake jawabi ga manema labarai na fadar shugaban ƙasa, shugaban hukumar ta FIRS ya ce bayan amincewar, matatun man na cikin gida za su dinga siyar da tataccen man ga ‘yan kasuwa domin amfani da shi a cikin ƙasar nan.