
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai, ya maka majalisar dokokin jihar Kaduna kara a kan zargin karkatar da naira biliyan 432 a gwamnatinsa na shekaru takwas, wanda ya bar jihar da dimbin bashin da ake bin sa.
El-Rufai ya kai karar majalisar dokokin jihar a gaban babbar kotun tarayya dake Kaduna a yau Laraba.
Karar, wacce lauyan tsohon gwamnan, Abdulhakeem Mustapha, babban lauyan Najeriya, SAN, ya shigar da karar, ya kalubalanci rahoton kwamitin majalisar Kaduna wanda ya tuhumi El-Rufai kan zargin almundahana.
A tuna cewa kwamitin wucin-gadi da majalisar dokokin jihar Kaduna ta kafa domin binciken duk wasu kudade da lamuni da kwangiloli da aka bayar karkashin Nasir El-Rufai ya mika rahotonsa inda ya tuhumi tsohon gwamnan da wasu daga cikin wadanda ya nada.
Sai dai El-Rufai, cikin gaggawar martanin da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Muyiwa Adekeye, ya yi ya kalubakanci rahoton, inda ya bayyana shi a matsayin karya da abin kunya.