Home Labarai DA ƊUMI-ƊUMI: Sojoji sun yi gargaɗi ga masu kiran juyin-milki a Nijeriya

DA ƊUMI-ƊUMI: Sojoji sun yi gargaɗi ga masu kiran juyin-milki a Nijeriya

0
DA ƊUMI-ƊUMI: Sojoji sun yi gargaɗi ga masu kiran juyin-milki a Nijeriya

Rundunar sojin Nijeriya ta yi gargadi ga masu kira da a yi juyin mulki saboda wahalhalun da ake fuskanta a kasar.

A halin yanzu, Najeriya na fuskantar matsalar tattalin arziki mafi muni a tarihi, lamarin da ya janyo zanga-zanga a sassa daban-daban na kasar.

Wasu dai na cewa idan ba a magance al’amura a kan lokaci ba, to sojoji za su iya hamɓarar da gwamnatin shugaba Bola Tinubu.

Da yake mayar da martani, babban hafsan hafsoshin tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya ce masu yin wannan kira ba sa kaunar kasar, yana mai gargadin cewa doka za ta yi aiki a kan su.

Musa ya ce rundunar sojin kasar za ta ci gaba da yin abin da ya kamata domin kare dimokuradiyyar kasar.

Daily Trust ta rawaito cewa Musa ya yi wannan jawabi ne a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai jim kadan bayan da ya kaddamar da babbar kofar shiga runduna ta 6, da sojojin Najeriya da na jami’an ‘yan sanda, dukkansu a hedikwatar shiyya da ke Port Harcourt, babban birnin jihar Rivers.

Yayin da ya amince cewa kasar na fuskantar kalubale, ya ce kiraye-kirayen juyin mulkin bai dace ba saboda kasashe suna samun ci gaba da sauri ne a karkashin tsarin dimokuradiyya..