
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannu kan dokar mafi ƙarancin albashi na Naira dubu 70.
Shugaban ƙasar ya sanya hannu ka ƙudurin dokar ne a yau Litinin bayan majalisar wakilai ta amince da ƙudurin.
Dokar dai ta amince da Naira dubu 70 a matsayin mafi karancin albashi ga ma’aikatan kasar nan.
Haka kuma ta amince a dinga bibiyar mafi ƙarancin albashin duk bayan shekaru 3 maimakon shekaru 5 a baya.