
Shugaban kasa Bola Tinubu yayi kira da shugabannin kasashen duniya da su bada muhimmanci wajen yafewa Nijeriya bashin da ake bin ta.
Shugaban kasar ya kuma bukaci majaisar dinkin duniya da ta bada muhimmanci ga alakar kasuwanci tsakanin kasashe ba tare da nuna bangaranci ba kamar yadda yake a tsarin shiga a dama da kowa da daidaito gami da hadin kai.
Tinubu wanda shi ne shugaban kungiyar ECOWAS ya yi kiran ne a jawabin da ya gabatar a zauren majalisar dinkin duniya a taron ta karo na 79 a birnin New York.
Shugaban kasar, wanda ya samu wakilcin mataimakin sa, Kashim Shettima, ya ce kasashen na kudancin duniya baza su samu ci gaban tattalin arziki ba idan ba a rage musu bashin da ake bin su ba.
A wata sanarwa da mai taimakawa shugaban kasa kan fannin kafafen yada labarai a ofishin mataimakin shugaban kasa, Stanley Nkwocha, ya ce shugaban Nijeriyar ya jawo hankalin shugabannin duniya kan yadda bashin da ake kasashe ke hana su biyan bukatun yan kasashen su.
A rahotan ofishin kula da basussuka na kasa, bashin da ake bin Nijeriya na cikin gida da na waje ta kai Naira Tiriliya 121.67.
Da yake jawabi kan kalubalen bashin, Tinubu ya ce, “Haka abin yake, dole ne mu tabbata duk wani garambuwl ga tsarin hada hadar kudade ya hada da rage matakan bashin da ake bi don bada dama wajen ayyukan ci gaba.
” Kasashen kudancin duniya baza su iya samun ci gaban tattalin arziki ba ba tare da an rage musu bashin da ake bin su ba”, inji shi.