Home Labarai Wakilan gidajen jaridu sun ƙaurace wa rahoton aiyukan gwamnatin Kano

Wakilan gidajen jaridu sun ƙaurace wa rahoton aiyukan gwamnatin Kano

0
Wakilan gidajen jaridu sun ƙaurace wa rahoton aiyukan gwamnatin Kano

Ƙungiyar wakilan jaridu, wacce ake kira ‘ Correspondents’ Chapel ‘ da ke ƙarƙashin ƙungiyar ƴan jarida ta Najeriya, NUJ, reshen jihar Kano ta ce za ta ƙaurace wa bayar da rahoto kan duk wasu ayyukan gwamnatin jihar Kano daga yau Litinin.

Ƙungiyar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta fitar yau, wadda ta samu sa hannun shugaban ta, Aminu Ahmed Garko.

Sanarwar ta ce ta ɗauki matakin ne sanadiyyar cin zarafin da jami’an gwamnatin jihar ta Kano ke yi wa wakilanta a lokacin da suke gudanar da ayyukansu.

Sanarwar ta ce “duk wani yunƙuri da aka yi na tattaunawa da gwamnati da jami’anta domin warware matsalolin abin ya ci tura”.

Sanarwar ta ci gaba da cewa wakilan kafafen yaɗa labarun sun ci gaba da fuskantar “hantara da tsangwama har ma da duka a lokacin da suke gudanar da ayyukansu”.

Daga nan sai sanarwar ta ce ƴan jaridar ba za su sake ɗaukan rahoton duk wani taron manema labaru, ko ayyukan gwamnati ko tattaunawa da jami’an gwamnatin ba har sai gwamnatin jihar ta ɗauki alƙawarin kare ƴanci da lafiyar ƴan jarida.

Najeriya na daga cikin ƙasashen da ake wa kallon masu rauni wajen kare hakkin ƴan jarida.

A cikin rahotonta na shekara ta 2023, ƙungiyar kare hakkin ƴan jarida ta Reporters Without Borders ta ce ƴan siyasa a ƙasashe irin Najeriya na amfani da ƙarfinsu wajen daƙile ayyukan ƴan jarida, yayin da kuma wasu ƴan siyasar ke kafa nasu kafafen yaɗa labarun domin yaɗa farfaganda da labaran bogi.

BBC Hausa