Home Labarai Ƙwararru sun shawarci CBN da ya sauƙaƙa rijistar BVN

Ƙwararru sun shawarci CBN da ya sauƙaƙa rijistar BVN

0
Ƙwararru sun shawarci CBN da ya sauƙaƙa rijistar BVN

Wani kwararre kuma Shugaban kamfanin hada-hadar kudade na zamani, Arvofinance, Ayotunde Bally, ya bukaci babban bankin kasa, CBN, da ya sauƙaƙa hanyoyin yin rijistar BVN.

Bally ya ba da shawarar ne a wata hira da kamfanin dillancin labarai na kasa, NAN, a yau Talata a Legas.

Shugaban ya bukaci hukumomi da su hada hannu da gidajen kaiwa da karbar sakonni, ko kungiyoyi masu zaman kansu da ke da fa’ida don samun hanyar da ta dace da yin rajistar BVN.

Ya kuma ba da shawarar binciko mafita na fasahar zamani don daidaita tsarin yin rajista don ya fi dacewa.

“Rufe duk asusun ajiya da basu da BVN babban mataki ne, sai dai kuma hakan ya haifar da matsaloli biyu. Mutanen da ba su da rajistar BVN, za su fuskanci matsala wajen shiga asusun ajiyarsu na banki, lamarin da zai iya janyo wahalhalu na kudi da cikas a rayuwarsu ta yau da kullum.

“Duk da cewa tura rajistar BVN ba wani mummunan mataki ba ne na magance zamba da kuma tabbatar da ingancin tsarin hada-hadar kudi, duk aikin rajistar BVN yana da tsauri.

“Don haka, me yasa ba za a sauƙaƙe ta hanyar haɗin gwiwa tare da ofisoshi ko ƙungiyoyi masu zaman kansu waɗanda ke da fa’ida a cikin yankunan karkara da kuma amfani da fasahar zamani ba?” in ji shi.