Daga Muhammad Bashir Amin

Wasu Matasa masu kaunar Dan takarar gwamna jihar Kano karkashin inuwar tutar Jam’iyyar PDP Mal. Salihu Sagir Takai Sun Tuko keke daga Kauyen Kachako Cikin Karamar hukumar Takai don jaddada goyan bayansu ga takarar Takai 2019.

Da Muke zantawa da Shugaban tawagar Mahaya Kekunan Nazifi Nagge Kachako, ya bayyana cewa sun tawo su uku akan Keke tun daga kauyensu Na Kachako kuma zasu koma akan Kake kamar yadda suka tawo, kuma sun ci Alwashin ci gaba da kawo irin wannan Ziyarar akan Kekunansu duk ranar Juma’a har sai an bayyana Takai a matsayin gwamnan jihar Kano a Zaben 2019, ya kuma ci gaba da cewa ba iya su kadai ba ne Kungiya ce da su guda, yanzu su Shugabannin ne suka fara bude kofa a yau Juma’a 31/08/2018.

Garin Kachako dai gari ne mai Nisan gaske zuwa cikin Birnin Kano wanda Akalla zaka iya kwashe tafiyar awa daya da minti Arba’in a mota.