Home Labarai Wata mata ta azabtar da ɗan kishiya saboda ya shanye ragowar shayin ɗanta

Wata mata ta azabtar da ɗan kishiya saboda ya shanye ragowar shayin ɗanta

0
Wata mata ta azabtar da ɗan kishiya saboda ya shanye ragowar shayin ɗanta

 

 

Wani yaro dan shekara 15 ya sha daku a hannun kishiyar mahaifiyarsa a Obiofia Nnewichi Umuezize, a Ƙaramar Hukumar Nnewi ta Arewa a jihar Anambra.

Jaridar The Nation ta rawaito cewa matar da yi wa yaron duka da karfe saboda ya sha ragowar shayin ɗan uwansa ya rage.

Jaridar ta tattaro cewa mahaifin yaron, Okwudili Ikediobi, shi ma ya ɗaure hannayensa da kafafunsa ta kuma kai shi gidan mari bayan ya samu labarin shan shayin, inda ya yi watsi da shi na kwanaki ba tare da bashi abinci ba.

Yaron da ya ke bayyana abin da ya faru da shi ya ce, “An fara cin zarafina ne a lokacin da aka dauke mu daga gidan yara na Ozubulu. An azabtar da ni sosai saboda na shanye ragowar shayin kani na wanda ya sa mahaifiyarsa ta doke ni da karfe.

“Nan da nan mahaifina ya ji abin da ya faru, sai ya daure hannuna da kafafuna ya kai ni gidan mari.

“An bar ni a can kwanaki ba abinci. Hatta ’yar’uwata, wadda takan sato jiki ta kawo mini abinci, ita ma sai da ta sha azaba sosai.”

Game da yadda ma’aikatan jin dadin jama’a suka cece shi, yaron ya ce, “a lokacin da na ke yawo bayan ‘yar’uwata ta taimaka min na tsere, wasu da suka ga raunukan da ke hannuna, suka fara yi min tambayoyi.”

Yanzu dai an mika batun ga ma’aikatar mata da walwalar jama’a.

Kwamishiniyar ma’aikatar, Ify Obinabo, wacce ma’aikatan jin dadin jama’a daga Nnewi suka sanar da hakan, ta ba da umarnin a kai shi Asibitin Koyarwa na Jami’ar Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu ko Asibitin Koyarwa na Jami’ar Amaku, Awka domin samun jinya cikin gaggawa.