
Wata mata mai juna biyu, a jiya Litinin ta haifi ɗa namiji a kan hanya a Legas.
Babban Sakatare na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Legas, LASEMA, Dokta Olufemi Oke-Osanyintolu, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar, ya ce mahaifiyar da jaririn na cikin koshin lafiya.
“A ranar 19 ga watan Fabrairu, da misalin karfe 9:00 na safe, tawagar bayar da agajin gaggawa ta hukumar ta samu kiran gaggawa daga Onipanu Bus Stop.
“Mun samu kiran ne game da wata mata mai juna biyu wacce ba zato ba tsammani ta shiga nakuda a tashar bas yayin da take jiran shiga mota.
“Nan da nan muka shirya mata shinge don kare ta da tabbatar da haihuwar jaririn lafiya,” in ji shi.
Ya ce matar, wacce ba a ambaci sunanta ba, ta samu nasarar haifo wani santalelen jariri, lamarin da ya sanya mutane ln da ke wajen su ka riƙa murna.
“Jami’an hukumar, bayan nan, sai suka garzaya da mai jegon da jaririn ta asibiti mafi kusa domin samun kulawar likitoci,” in ji shi.