Sarkin Kano Muhammadu Sunusi na biyu
Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi na biyu ya bayar da Shawarar a dinga yiwa Sarakuna da Gwamnoni da masu neman tsayawa takara gwajin ko suna shan kayan maye.
Sarkin yace, a shirye yake a gwada shi domin tabbatar da ko yana ta’amuli da kayan maye ko a’a. Sarkin ya bayyana hakan ne, a wani taron yini biyu da ake yi a jihar Kano domin magance matsalar shaye shayen miyagun kwayoyi da ya addabi matasa maza da mata a Arewacin Najeriya.
Taron dai ofishin Shugaban majalisar dattawa Sanata Bukola Saraki ne ya shirya shi, domin nemo bakin zaren rage ko dakile matsalar shaye shayen miyagun kwayoyin da suka addabi matasa a Arewacin Najeriya.
Ko yaya kuke kallon wannan shawara ta Sarkin Kano?