YAKAMATA A CANJA SUNAN KOFIN ZAKARUN TURAI YA KOMA SUNANA, CEWAR RONALDO

Daga Abba Ibrahim Wada Gwale

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Cristiano Ronaldo, dan kasar Portugal, ya bayyana cewa ya kamata hukumar kwallon kafa ta nahiyar turai ta canja sunan kofin zakarun turai daga champions league zuwa CR7 champions league.

Ronaldo ya bayyana hakane a hirarsa da manema labarai bayan da kungiyarsa ta Real Madrid ta samu damar lashe kofin karo na 13 a tarihi kuma karo na 3 a jere a hannun kungiyar Liverpool daci 3-1 a kasar Ukraine.

Lokacin da aka tambayi dan wasan cewa ko ya ji haushi da har aka kammala wasan bai zura kwallo a raga ba kuma kungiyarsa ta samu nasara sai yace sam baiji haushi  ba, hasali ma yakamata a canja sunan kofin zuwa sunansa.

Ronaldo ya ce yakamata sunan kofin ya koma sunansa saboda yafi kowanne dan wasa lashe kofin a tarihi sannan kuma ya yafi kowanne dan wasa zura kwallo a raga a tarihin gasar sabida yanada kwallaye 120 kawo yanzu.

A yanzu dai Ronaldo yana bukatar ya lashe kofin sau daya domin ya kamo tsohon dan wasan kungiyar wato Francisco Gento, wanda yataba lashe kofin sau shida a tarihi yanzu kuma yanada guda biyar.