Daga Zaidu Bala

Ma’aikatan Jihar Kebbi suma sunbi Takwarorinsu wurin Gudanarda Bukin Ranar Ma’aikata ta Duniya Kuma Bukin ya Gudana a Haliru Abdu Stadium dake Birnin Kebbi, kuma an gudanarda Bukin Karkashin Jagorancin Shugaban Kungiyar Kwadigo na Jihar Kebbi Comrd. Umar Haliru Alhassan.

Kuma Bukin ya samu halartar Kungiyoyin Kwadigo daban Daban wadanda Sunka hada da NLC, NULGE, TUC, NUJ, NUT, ASCSN, NCSU. SSANU, Da dai sauransu.

Inda taron ya samu wakilcin Maigirma Gwamnan Jihar Kebbi Sen. Atiku Bagudu wanda Sekataren Gwamnatin Jihar Kebbi Alh. Babale Umar ya wakilta, inda Gwamnatin Jihar Kebbi tace Shirye take ta biyaba Ma’aikatan Jihar Kebbi bukatunsu Don samun cigaban Jihar Kebbi.

Daga Zaidu Bala Kofa Sabuwa Birnin Kebbi