Home Labarai Yadda gwamnan Neja ya bada umarnin a daki wani malami a wajen zaman makoki

Yadda gwamnan Neja ya bada umarnin a daki wani malami a wajen zaman makoki

0
Yadda gwamnan Neja ya bada umarnin a daki wani malami a wajen zaman makoki

An ga Gwamnan jihar Neja, Umar Bago, a wani faifan bidiyo, na baiwa jami’an tsaron sa umarnin su mammari wani malamin addini.

A bidiyo, an hango gwamnan na bada umarnin a kama tare da karantar da malamin dan kawai ya nemi ya yi addu’ar rufe taro.

Daily Nigerian ta biyo cewa lamarin ya faru ne a wajen addu’ar ukun matar mataimakin gwamnan jihar, marigayiya Zainab Yakubu Garba a Minna.

A faifan bidiyon da Daily Nigerian ta samu, an ga Gwamnan zaune a cikin masu zaman makoki, inda ya bada umarnin wani ya yi wa marigayiyar addu’a.

Sai shi wannan malamin ya nuna cewa shi zai yi addu’ar, lamarin da ya ɓata wa Bago rai har ya ke tambayar sa cewa “kai malami ne to?”

Nan da nan sai gwamnan ya baiwa jami’an tsaron da ke wajen umarnin su dadume malamin.

“Ku mare shi !!, ku mammare shi na ce!!. Ku kama shi ku tafi da shi!! Ku ladabtar da shi sannan ku dawo da shi!!, in ji shi.