Bello Galadanchi, Shugaban Kasuwar Bello ta yanar gizo

DAILY NIGERIAN ta zanta da Shugaban kasuwar Bello, kasuwa irinta ta farko a shafukan yanar gizo da Hausa, wadda Bello Galadanchi PhD ya kirkira, inda kuma yake gudanar da hada hadar kasuwancin nasa duk a kafar sadarwa ta intanet.

Bello ya bayyana mana yadda suka samu tagomashi cikin kankanin lokaci a yanayin kasuwancin da suke yi a kasuwar Bello. Ya kuma bayyana mana yadda suka yi cinikin miliyoyin kudade a cikin kankanin lokaci:

“Kasuwar Bello ta fara hada-hadar sayar da kaya a tsarin kasuwanci gabannin watan azumi saboda neman albarkar wannan lokaci, da kuma fahimtar bukatar jama’a gabannin Sallah. To jama’a daga duka jihohin arewacin Najeriya masu yawa sun yi cinikin kaya ta shafukan Kasuwar Bello dake yanar gizo da WhatsApp, da Facebook da Instagram, da ma ta wayar tarho.”

“Tsarin Kasuwar shine saya wa jama’a irin kayan da suke so a China, a tura musu har jihohin su kyauta a farashi mai ban mamaki. Misali, jakar dubu biyar a Kasuwa ana samun ta a dubu biya a Kasuwar Bello, haka zalika rigunan yara na dubu biyar akan same su a dubu daya da dari biyar. Bello Galadanchi Ph.D wanda ya kirkiri kasuwar ya fahimci bukatun masu karamin karfi, shiyasa ya shirya tsare tsaren da zai samar da kayan Sallah ga masu bukatar sari akan farashi mai rahusar gaske, da har ta kai wasu kwastomominsa suna rera mishi wakoki saboda murna.”

“A cikin watanni da bude hada-hadar kasuwanci, Kasuwar Bello ta sayar da rigunan yara mata dubu huda da dari takwas da sittin da shida (4865) da takalman yara kafa dubu uku da dari takwas da ashirin da biyar (3825) da leggings dubu biyu da dari bakwai da saba’in da biyar (2775), da takalman mata dubu biyu da tamanin da shida (2086). Banda su akwai kaya masu yawa kamar jakunkunan mata da kayan wutar lantarki da kayan wasa da suma aka yi cinikinsu. A takaice Kasuwar tayi cinikin sama da Nera miliyan 30 a cikin watanni biyu.”

“Idan kayan suka isa Lagos daga China, agents din Kasuwar Mudassir Mande da Alhaji Arzeka zasu tarbe su sannan su tura su Kano wajen Super Agent Yaya Abubakar da Haruna Shu’aibu Danzomo da Muhammad Sulaiman Labbo. Daga nan za’a kaisu warehouse din Kasuwa a sharada inda za’a tantance su, sannan a ware su domin turawa agents din jihohi daban daban da kwastomomi a duk arewacin Najeriya.” A cewar Shugaban Kasuwar Bello, Mallam Bello Galadanchi PhD.