Mambobin kungiyar masu fama da cutar Sikila ko kuma Sankarar Jini suka bayyana, yadda wasu ‘ya ‘yan kungiyar 30 suka mutu a watan Oktoba saka makon karancin jini.

Da yake zantawa da manema labarai, Sakataren kungiyar, Abdulkadir Ibrahim, ya bayyana cewar, masu dauke da cutar sun mutu ne a sanadiyar tsananin bukatar karin jini da suke da ita, domin tsira da rayuwarsu, amma hakan bai samu ba, sabida an samu karancin jinin da za’a kara musu.

Ya kara da cewar, rasuwar masu dauke da wannan cuta, ya sanya kungiyar shirya gangamin bayar da tallafin jini ga masu dauke da cutar a ranar 29 ga watan Oktoban da ya shude, tre da nuna jin jina ga wadan da suka bayar da jininsu domin taimakawa masu dauke da wannan cuta.

Ya cigaba da cewar, an kafa kungiyar masu fama da cutar Sankarar Jini shekaru 25 da suka wuce, wanda a halin yanzu suke fama da tarin matsaloli da suka hada da na kudi da kuma karancin masu bayar da tallafin jini, wanda hakan ya janyo mutuwar masu dauke da cutar da dama.

“A watan Oktoba kawai da ya gabata, mutum 30 masu dauke da wannan cuta ne suka mutu, sakamkon fuskantar karancin jini da kuma tsananin bukatarsa da suke yi, kuma wadannan da suka rasu sune kadai mutanan da suka yi rijista da kungiyarmu, a asibitin kwararru na Murtala”

“Wannan shi ne, babban dalilin da ya sanya muka kaddamar da gangamin bayar da tallafin jini ga masu dauke da wannan cuta, kuma Alhamdulillah, mutane da dama sun amsa wannan kira, sun bayar da tallafin jini, amma duk da haka muna bukatar a sake bayarwa sosai, musamman a wannan lokacin na hunturu da aka fi bukatarsa”

“A sabida haka,a muke kara rokon jama’a da su taimaka wajen bayar da tallafin jininsu don taimakon masu dauke da wannan cutar, sabida da yawan masu dauke da ita, ba zasu iya sayan jini a yi musu kari ba, sabida rashin kudi.”

Bayan haka kuma, Abdulkadir, yayi kira ga Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje da ya taimakawa ‘ya ‘yan wannan kungiya musamman a yanzu da suke fuskantar tarin matsaloli. Kanan kuma, yayi kira ga masu hannu da shuni da su ma, su taimakawa masu dauke da wannan cutar, domin kare rayukan yara da matasa daga salwanta sakamakon wannan cuta.

A karshe yace, masu dauke da cutar Sankarar jini ko Sikila, suna bukatar kulawar likitoci a koda yaushe, tare da bukatar cin abinci mai gina jiki, amma sabida karancin kudi da kuma halin matsi da ake ciki, yasa masu dauke da cutar suke fuskantar barazana da yawa.