Gasar tsere mai nisan zango karo na uku da ake kira a turance da Lagos City Marathon na bana ya fara da misalin karfe 6:30 na safiyar yau Asabar.

Tsohon kyaftin din tawagar kwallon kafa ta Nijeriya, Austin Jay-Jay Okocha da takwaransa na tawagar kwallon kwandon Nijeriya, Olumide Oyedeji sun halarci wajen mika kyaututtukan ga wadanda suka yi nasarar lashe gasar ta bana, kuma sun yabawa wadanda suka shirya gasar tseren da ma duk wadanda suka bayar da gudunmawarsu wajen ganin gasar ta bana ta yi nasara.

Tseren da zangonsa kilomita 42 ne ya fara ne daga filin wasanni na kasa da ke Surelere inda ya kare a Eko Atlantic.

Taron na bana ya samu akalla mutane 100,000 da suka shiga gasar, wanda Okocha ya bayyana cewa wannan ba karamin ci gaba bane ga ci gaban harkar wasanni a kasar Nijeriya.

 Bafuranshe, Abraham Kiprotich, ne ya lashe gasar ta bana wacce bankin Access ya dauki nauyi. Kiprotich, wanda haifafen kasar Kenya ne kuma mai shekaru 32, ya kammala kilomita 42nsa a cikin awanni 2 da mintina 15 da sakan 4. Wannan ya bashi damar lashe kyautar dalar Amurka dubu 50 da aka sanya za a bawa duk wanda ya lashe gasar.
Iliya Pam, shi ne dan Nijeriyan da ya zo na daya a kafatanin ‘yan Nijeriyan da suka shiga gasar. Iliya, ya shanye kilomita 42 a cikin awanni 2 da mintuna 27

A yayin mika kyautukan, Gwamnan jihar Legas, Akinwunmi Ambode ya bayyana cewa, “Har yanzu matsayin shirya gasar bai kai yadda jihar ta ke so ba, tunda bai kai yadda manyan kasashen duniya suke shirya nasu ba, amma nan da shekaru biyu masu zuwa, za mu kai inda muke burin kaiwa.”

“Mun gaji da mika kyautar gasar ga ‘yan Afirka ta gabas a duk shekara. Saboda haka za mu horar da masu tserenmu na gida Nijeriya ta yadda suma za su dinga yin nasara a gasa irin wannan,” inji Ambode.