Shafiu Garba, Mahaucin da soja ya harbe har lahira a jihar Edo

Wani soja mai suna Sunday ya kashe wani Bahaushe mai sana’ar fawa. Shafiu Garba ya gamu da ajalinsa ne, a lokacin da motar su ta shallake shingen jami’an tsaro a jihar Edo ba tare da sun bayar da cin-hancin naira 500 ba.

Al’amarin ya faru ne, a lokacin da Shafi’u Garba, wanda aka fi sani da Ganda, ya dauko shanu a mota daga garin Wudil dake jihar Kano zuwa jihar Edo a kudu maso kudancin Najeriya.

Wanda abin ya faru a kan idonsa ya bayyana mana, cewar a wani shingen jami’an tsaro ne dake Uromi wani gare da yake tsakanin Auchi da Benin, da misalin karfe 6 na yamma a ranar 8 ga watan Disamba.

Shaidar, Abdullahi Sani, wanda yana cikin motar tare da Shafiu Garba, yace sojan ya harbi Garba aka, kuma ya rasu ‘yan awanni bayan faruwar lamarin.

“Bayan da muka taho, mun gota shingen jami’an tsaron, sai muka lura da wani soja na binmu a guje akan babur, marigayi Shafiu Garba, shi ne yace mu tsaya tunda ya fahimci sojan mu yake bi a guje”

“A lokacin da muka tsaya, sojan ba tare da wata wata ba, ya saita mu da bindiga, ya harba bindiga sama, harsashi na farko ya daki saman motarmu, sannan,  harsashi na biyu shi ne ya samu Shafiu Garba a kansa”

“A lokacin da muka taho, babu wanda ya nuna mana alamun mu tsaya a shingen jami’an tsaron. Kawai dai mun lura da soja da yake binmu a guje akan babur, daga nan muka ji yana harbi, yana fadin me ysa muka wuce bamu ajiye 500 din da ake ajiyewa ba”

“An garzaya da Shafiu Garba wani asibiti dake kusa, amma ba’a iya ceto rayuwarsa ba, domin ya rasu ‘yan awanni bayan harbin da aka yi masa. Mun shigar da koken abinda ya faru gaban baturen ‘yan sanda na Uromi,amma sai ‘yan sandan suka nemi cakuda takardu”

“Daga nan, muka fusta shi ne muka fitomuka tare hanya washegarin ranar da abin ya faru, muna kiran san am bi kadun wannan bawan Allah. Mun kuma nemi da a mayar da gawarsa Arewa domin yi mata suturar da ta dace”

“Duk da cewar, sojoji su ne suka biya dukkan kudaden da asibitin ya caza dangane da Shafiu Garba. Amma wannan ba shi ne abinda muka bukata ba, so muke a yi mana adalci, shi wancan soja da yayi wannan kisa a yi masa hukunci daidai da abinda ya aikata” A cewar wanda abin ya faru akan idonsa.

Bayan haka kuma, DAILY NIGERIAN ta nemi jin ta bakin kakakin rundunar tsaron sojoji ta Najeriya Kanar Sani Usman Kukasheka akan wannan batu, yace shima an turo masa da sakon faruwar lamarin ta tes.

Amma har ya zuwa lokacin hada wannan rahoto Kukasheka bai mayar da jawabi ba kan wannan batu, sannan kuma bai mayar da martani ba akn sakon tes da aka aika masa a wayarsa.

1 COMMENT