Home Ilimi Yajin Aiki: Za mu ɗauki mataki a kan gwamnati nan da awa 48- ASUU

Yajin Aiki: Za mu ɗauki mataki a kan gwamnati nan da awa 48- ASUU

0
Yajin Aiki: Za mu ɗauki mataki a kan gwamnati nan da awa 48- ASUU

 

Da yiwuwar Ƙungiyar Malaman Jami’a, ASUU ta kuma tafiya yajin aikin sai-baba-ta-gani bayan da ta ce za ta dauki matakin da ya dace a kan gwamnatin Nijeriya nan da kwanaki biyu masu zuwa.

Shugaban ASUU na ƙasa, Farfesa Emmanuel Osodeke ne ya bayyana haka a tattaunawarsa da Jaridar Daily Trust ta wayar tarho a yau Litinin.

Farfesa Osodeke ya baiyana cewa za su ɗauki matakin ne sabo da gwamnatin ta gaza cika alƙawuran da ta ɗauka a kan biyan buƙatun ƙungiyar.

Shugaban kungiyar ya ce ”Za su zartar da hukuncin da ya dace a ranar Laraba tare da sanar da dukkanin sauran mambobinta matsayarta game da gwamnatin tarayya” Inji Farfesa Osodeke.

Idan ba a manta ba, a ranar 14 ga watan Oktoba ne ASUU da Ministan Kwadago, Chris Ngige suka gana tare da tattaunawa kan cika alkawuran da gwamnatin tarayya ta daukar musu.

Daga cikin matsalolin da suka tattauna akwai bukatar yih gyare-gyare a wasu jami’o’in kasar nan da kuma biyan alawus din malamai.

Kazalika, an tattauna wasu alkawura da aka yi wa kungiyar tun a shekarar 2009 da kuma tsarin biyan albashin ma’aikata na IPPIS da kungiyar take adawa da shi.