33.1 C
Abuja
Saturday, November 26, 2022

Yajin aiki: Mambobin mu 10 ne su ka rasu — ASUU

Must read

 

A kalla mambobin kungiyar malaman jami’o’i, ASUU, reshen jami’ar Calabar 10 ne suka mutu a yajin aikin da suka fara a ranar 14 ga watan Fabrairun 2022.

Daily Trust ta rawaito cewa shugaban ASUU na jami’ar, Dr John Edor ya ce malaman da su ka rasu sun haɗa da farfesoshi biyar, ya kara da cewa ba gaskiya ba ne hukumar ta rasa malamai 21 kamar yadda rahotanni su ka nuna da farko.

Edor ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar a yau Laraba, sai dai ya ce kungiyar ba za ta yi karaya wajen ci gaba da fafutukar neman hakkinsu ba.

Ya ce, “Ba daidai ba ne cewa mambobin kungiyarmu 21 da ke Jami’ar Calabar sun rasa rayukansu a sakamakon yajin aikin nan.

“Zan iya tabbatar da cewa mun rasa kusan mambobinmu 10, amma ba duka ne farfesoshi ba. Sun haɗa da Farfesa Gabriel U. Ntamu, Farfesa Judith Otu, Farfesa Udosen, Farfesa Kate Agbor, Farfesa Obia da sauran malaman jami’o’i.

“Duk da rashin kulawa da tursasawa da Gwamnatin Tarayya ke yi, ba za mu karaya wajen neman hakkokin mu ba.

“Duk da cewa gwamnati ta ki sauraron halin da muke ciki tare da samar da ingantacciyar hanya ba tare da cikas ba, za mu ci gaba da jure duk asarar da muka yi sanadiyar yajin aikin.

“Mu na sane da yunwa, tsoratarwa ko umarnin kotu. Ba gudu ba ja da baya a wannan yaki. Za mu kai shi har ƙarshe inda gwamnati za ta yi abubuwan da ya kamata ta yi.

 

More articles

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Latest article

- Website Designed By DEBORIAN.COM, a Nigerian Web Designer and Web Developer -