
Idan ba wani sauyi a ka samu ba, a ranar Laraba ne ma’aikatan wutar lantarkin Najeriya da ke karkashin kungiyar ma’aikatan wutar lantarki ta kasa, NUEE, za su fara yajin aikin sai baba-ta-gani a r kan matsalolinsu da kamfanin rarraba wutar lantarki ma na ƙasa, TCN bai warware musu ba.
Wata takardar da aka sanya wa hannu a yau Litinin da Babban Sakataren NUEE, Joe Ajaero, mai taken “jan hankali”, ya umarci manyan sakatarorin kungiyar na ƙasa da na shiyya-shiyya da su tabbatar sun bi umarnin yajin aikin.
Sanarwar ta kuma umurci ma’aikatan da su yi wa hedikwatar TCN ta kasa Abuja tsinke ranar Talata.
rahotanni sun ce matakin yajin aikin zai jefa kasar cikin wani mawuyacin hali na rashin wutar lantarki.
Ko a ranar 20 ga watan Yuli, layin rarraba wutar lantarki na kasa ne ya sauka, lamarin da ya jefa sassa da dama na kasar cikin duhu.
A lokacin da aka katse, a cikin dukkan kamfanonin rarraba wutar lantarki, Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Abuja, AEDC ne kawai ya samu 40MW a wancan lokacin tare da wasu ma na da 0MW.