27.7 C
Abuja
Tuesday, January 25, 2022

Yajin Aikin ƴan Adaidaita-sahu: Ƴan Sanda sun kama mutane 40 a Kano

Must read

 

 

Rundunar Ƴan Sanda ta Jihar Kano ta ce ta kama kimanin mutane 40 bisa zargin afkawa wasu masu sana’ar babur mai ƙafa uku, wanda a ka fi sani da Adaidaita-sahu a jihar, sabo da ƙin shiga yajin aikin da su ke yi.

Rundunar ta kuma ce waɗanda a ke zargin sun kuma yi wa masu tafiya a ƙafa ƙwace.

Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya baiyana hakan ga manema labarai a jiya Litinin.

A cewar SP Kiyawa, mutanen da su ka kama suna ɗauke da makamai, inda su ke tare hanya su na yi wa mutane ƙwace da tilastawa masu ƙananan motoci ɗaukar kaya da sauke mutanen da suka ɗauko don rage musu hanya.

Ya ƙara da cewa an kama waɗanda a ke zargin ɗauke da adduna da gorori da sauran muggan makamai inda su ka haɗa cunkoso a tituna da kuka yi wa bayin Allah ƙwace.

Kiyawa ya ce ” da ga samun wannan rahoto, Kwamishinan Ƴan Sanda, Sama’ila Shu’aibu Dikko yai maza ya raba jami’an mu gurare daban-daban da mu ka samu rahoton, inda da ga haka ne har mu ka kamo mutane 40,”

Kakakin ya ƙara da cewa duk da cewa kundin tsarin mulkin ƙasar nan ya bada damar a yi zanga-zanga ta lumana, hakan ba zai zama hujja ta fakewa da ita a aikata laifuka ba.

Ya ƙara da cewa rundunar ba za ta naɗe hannu ta na kallon a na karya doka ta ƙyale ba, inda ya kira jami’an su da su kasance cikin shiri domin daƙile yiwuwar faruwar karya doka da oda a jihar.

More articles

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Latest article