27.7 C
Abuja
Tuesday, January 25, 2022

Yajin aikin adaidaita-sahu: Gwamnatin Kano za ta ƙaddamar da sabon tsarin sufuri

Must read

Gwamnatin Jihar Kano ta ce nan ba da jimawa ba gwamnatin za ta ƙaddamar da sabon tsarin sufuri a cikin babban birnin jihar.
Shugaban Hukumar kula Harkokin Sufuri ta Kano, KAROTA, Baffa Babba-Dan’agundi ne ya baiyana hakan
a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai kan tsawaita yajin aikin da masu adaidaita sahu su ke yi a Kano.
 “Gwamnati za ta ƙaddamar da sabon tsarin sufurin ne saboda muna son a duba yadda ake tafiyar da harkokin sufuri kamar yadda ake yi a yanzu.
 “Tuni dai shirye-shirye sun nisa wajen samar da ababen hawa.
 “Duk da cewa wasu sun biya kuɗaɗen da ya kamata, amma wasu kuma ba sa son biyan kuɗaɗen harajin gwamnati, kuma doka ta ce su biya.
 “Yan adaidaita wasun su ba sa son mutunta doka, su na ganin tsaron da suke samu a banza ne kawai”.
 “Ba ni da wani ikon cewa dole su koma aiki haka suma ba su da hurumin fadawa gwamnati abin da zata yi,” In ji Dan’agundi.
 Dan’agundi ya ce gwamnati ta damu da tsaro ba wai batun kudaden shiga ba kawai.
 “Wasu daga cikinsu su na aikata laifuka da baburan nasu, shi yasa ba sa son yin rajista,” in ji shi.
 Ya kuma ce Gwamna Abdullahi Ganduje ya umarci hukumar da ta taimaka wa wadanda a ka lalata musu baburansu saboda sun ki yadda su ki shiga yajin aikin.

More articles

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Latest article